Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Su Na Kai Farmaki Yanzu Haka A Bisichi Dake Karamar Hukumar Barikin Ladi


Rahotannin dake fitowa daga Jihar Filato na fadin cewa wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba su na kai farmaki da bindigogi yanzu haka a kan kauyen Bisichi dake karamar hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato

Wadanda aka samu magana da su ta waya daga kauyen sun ce har yanzu babu wani jami'in tsaron da ya je shi, kuma duk yunkurin da suka yi na neman taimako daga sojoji ko 'yan sanda ya ci tura.

Wannan kauyen dai akasarin mazaunansa manoma ne.

XS
SM
MD
LG