Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Fadi Lambar Rigar da Falcao Zai Sanya


Radamel Falcao
Radamel Falcao

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana cewa Radamel Falcao, zai sanya rigar tamaula mai lamba 9 a sabuwar kakar kwallon da aka shiga.

A farkon watan nan na Yuli ne dan wasan dan kasar Colombia ya koma kungiyar zakarun kwallon Firimiya Lig ta Ingila a zaman dan wasa na aro ko haya, amma nan gaba cikin wannan watan zai hadu da sauran sabbin abokan wasansa da zasu yi rangadin Amurka. Kungiyar ta kara masa hutu ne a saboda ya shiga cikin gasar cin kofin Copa America.

Fernando Torres shi ne ya sanya rigar tamaula mai lamba 9 a lokacin da yake Chelsea kafin ya koma AC Milan a watan Agustar bara.

haka kuma, Chelsea ta tabbatar da cewa sabon dan wasanta Asmir Begovic shi ne zai gaji riga mai lamba 1 a bayan da Petr Cech ya canja sheka zuwa kungiyar Arsenal.

Thibaut Courtois zai ci gaba da sanya riga mai lamba ta 13.

XS
SM
MD
LG