Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Mawakan Blues BB King Ya Rasu


Shahararren mawakin nan na Amurka, BB King, wanda ake dauka a zaman daya daga cikin wadanda suka fi lakance yadda ake kada Jita, kuma mawakin nau'in wakokin Blues da yafi suna a duniyal, ya rasu yana da shekaru 89 da haihuwa.

Lauyansa ya bayar da sanarwar cewa BB King, wanda ake masa lakabi da sunan Sarkin (mawakan) Blues "King of Blues", ya rasu cikin barci a gidansa dake birnin Las Vegas.

A cikin shekaru kusan 70 da BB King ya shafe yana waka, ya taimaka wajen fito da nau'in wakar Blues, ya kuma yi tasiri tare da zamowa abin koyi ga mawakan Blues da Rock a saboda yanayin muryarsa da kuma yadda yake gabatar da wakokinsa cikin hali na susar zuciya. Babu wani mawakin da ya kamo kafarsa wajen iya kada Jita.

Sunansa na ainihi dai shi ne Riley B. King, kuma an haife shi a wata gonar auduga dake Jihar Mississippi ta Amurka a shekarar 1925. Ya fara shiga wannan harkar waka ta hanyar zamowa DJ da kuma gabatar da wakoki a wani gidan rediyon dake garin Memphis a Jihar Tennessee, inda aka rika kiransa da sunan "Beale Street Blues Boy" wanda shi ne daga baya aka takaita aka maida "B.B."

An shigar da BB King cikin Dakin Gwarzayen wakoki na Rock & Roll da kuma Blues. Wakokinsa dxa suka yi fice, sun hada har da "The Thrill is Gone," "Let the Good Times Roll" da kuma "How Blue Can You Get."

XS
SM
MD
LG