Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bidiyon Sabuwar Wakar Rashin Yarda Da Kin Jinin 'Yan Kasashen Waje


Kungiyar mawakan nan ta Afirka ta Kudu mai suna Ladysmith Black Mambazo, ta fito da bidiyon wata sabuwar wakar da ta yi ta nuna kyama ga hare-haren da ake kaiwa kan 'yan kasashen waje dake kasar.

Kungiyar ta Ladysmith Black Mambazo ta hada kai da wasu mawaka irinsu Salif Keita domin nunawa 'yan Afirka da kuma duniya baki daya, cewa dukkan 'yan Afirka, uwarsu daya, ubansu daya, a ko ina suke zaune a duniya.

Yau Jumma'a aka sako wannan faifan bidiyo.

A yi kallo lafiya.

XS
SM
MD
LG