Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Matasa Su Kara Azama Wurin Tabbatar Da Kwanciyar Hankali A Zaben Gwamna


Matasa na murnar cin zaben Buhari cikin kwanciyar hankali
Matasa na murnar cin zaben Buhari cikin kwanciyar hankali

Yayin da zabukan gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jahohi ke kara karatowa, wani matashi mai suna Mohammed Awwal na kungiyar ankarar da matasa a siyasance, ya ce wajibi ne matasa su ribanya irin himmar da su ka bayar a baya, ta tabbatar da zaman lafiya, musamman ma a wasu jahohi masu sarkakkiya.

Awwal ya ce matasa da kungiyoyin sa kai a jahohin Kaduna da Kano da Gombe da sauran jahohi masu sarkakkiya na da aiki matuka na tabbatar da zaman lafiya, ganin yadda ake da wasu batutuwa a kasa.

Ya ce bai kamata matasa su yadda a yi amfani da su wajen tayar da hankali ba. To amma ya yaba da rawar da matasan su ka taka a zaben Shugaban kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:21 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG