Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kai Hari A Bajoga, Amma Maharan Kawai Suka Mutu


Bama-baman da aka samu makon jiya cikin wata motar da ta yi niyyar kai hari kan sojoji a Bajoga, Jihar Gombe, Nigeria
Bama-baman da aka samu makon jiya cikin wata motar da ta yi niyyar kai hari kan sojoji a Bajoga, Jihar Gombe, Nigeria

Rahotanni daga garin bajoga a Jihar Gombe na fadin cewa dazu da maraice ne aka ji karar fashewar wani abu a arewa da gari, daidai inda sojoji suke binciken ababen hawa masu zuwa Bajoga ko garin Ashaka.

Wani mazaunin garin na Bajoga ya ambaci wadanda suka ga wannan lamari da idanunsu su na fadin cewa wata mota ce dauke da mutane biyu ta fashe a dab da wurin binciken ababen hawan, kuma an ce tana dauke da mutane biyu cikinta.

Akwai rahotannin da ba a tabbatar da su ba dake cewa mutane biyun dake cikin wannan mota ne suka mutu, soja guda daya kuma ya ji rauni.

Idan ba a manta ba, wata motar da aka dasa bama-bamai cikinta ta yi kokarin tarwatsa wannan wurin binciken ababen hawa, amma kuma bama-baman ba su ta shi ba. Sojoji sun samu nasarar bindige maharin a wancan lokaci.

Zamu kawo muku karin bayani da zarar mun samu.

XS
SM
MD
LG