Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwa 10 Da Suka Girgiza Duniyar Kwallo A 2014: Na 10 - Kwallaye 4 Da Berardi Ya Jefa A Ragar AC Milan


Domenico Berardi (hagu) na kungiyar Sassuolo yana murna tare da Marcello Gazzola a bayan da ya jefa kwallo a ragar AC Milan
Domenico Berardi (hagu) na kungiyar Sassuolo yana murna tare da Marcello Gazzola a bayan da ya jefa kwallo a ragar AC Milan

Yau zamu fara duba abubuwa guda 10 da suka zamo na mamaki a fagen kwallon kafar duniya a shekarar 2014, kuma zamu faro da abinda editocin GOAL.COM suka zaba a matsayin na 10. Idan mai karanta wannan yana da nasa, to ya rubuto mana.

Domenico Berardi, mai shekaru 20 kacal, kuma dan wasan kungiyar Sassuolo, ya jefa dukkan kwallaye guda 4 a lokacin da kungiyarsa ta doke AC Milan da ci 4-3. Shi dayansa.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 80 da matashi mai irin wannan shekaru ya jefa kwallaye har guda 4 a wani wasa na lig-lig na kasar Italiya da ake kira "Serie A"

Kuma a sakamakon wannan wasa, kungiyar AC Milan ta kori manajanta na wancan lokacin, Massimilano Allegri, wanda yanzu yake manajan kungiyar Juventus.

A gobe zamu bayyana abu na 9 da ya girgiza duniyar kwallon kafa.

XS
SM
MD
LG