Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Michael Babatunde Yana Sha'awar Sake Komowa Super Eagles


Michael Babatunde na Najeriya
Michael Babatunde na Najeriya

Micahel Babatunde ya bayyana cewa a shirye yake ya komo cikin ‘yan kungiyar Super Eagles ta Najeriya.

Shekaranjiya laraba dan wasan na tsakiya ya cika shekaru 22 da haihuwa, kuma rabonsa da ya buga ma Najeriya kwallo tun lokacin da ya ji ciwo a hannu lokacin da Najeriya take bugawa da Argentina a gasar cin kofin duniya a kasar Brazil.

Babatunde yace garau yake ji yanzu, yana mai cewa fagen tamaula, fage ne da dan wasa ke nuna kwarewa da bajimtarsa, kuma dole ne kwach ya nemi wadanda suka dace da wani gurbi idan wasu ‘yan wasan bas u nan ko sun ji rauni.

Yace ba ya da damuwar cewa zai yi hasarar gurbinsa a kungiyar Super Eagles, amma yace kalubale ne a gare shi da ya kara kaimi da hazaka ta yadda masu kula da kungiyar ta kasa zasu gayyace shi.

XS
SM
MD
LG