Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Messi, Yaya Toure, Aguero Su Na Iya Komawa Sabbin Kulob


Shin tana yiwuwa Lionel Messi ko Arturo Vidal ko Sergio Aguero ko kuma Yaya Toure su canja kulob a wannan sabuwar shekarar da zamu shiga?

Rahotanni daga na kusa da Messi na fadin cewa watakila dan wasan yana tunanin barin FC Barcelona a shekara mai zuwa. Tambayar ita ce shin akwai wata kulob dake da kudin da zata iya sayen wannan dan wasa?

Shi kuwa Arturo Vidal an ce Manchester United tana sha'awar dauke shi daga Juventus, sai dai matsalar itace ciwon guiwar dake damunsa.

Akwai rade-radin cewa Sergio Aguero yana kwadayin lashe gasar cin kofin zakarun kulob na Turai, amma yana da wuya ya iya yin hakan a Manchester City a yanzu. An ce kungiyoyin dake zawarcinsa sun hada da Real Madrid da FC Barcelona.

Yaya Toure kuwa, bai boye ma kowa cewa bai ji dadin rawar da yake takawa yanzu a kungiyar Manchester City ba, kuma akwai rade-radin cewa kungiyar PSG ta Faransa tana sha'awar sayensa.

Sauran ‘yan wasan da ake rade radin cewa suna shirin barin kungiyoyinsu sun hada da David de Gea na Manchester United, da Marco Reus na Borussia Dortmund, da Paul Pogba na Juventus, da Edinson Cavani na PSG wanda Zlatan Ibrahimovic ya sha masa gaba a kungiyar, da kuma Ross Barkley na Everton.

XS
SM
MD
LG