Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Labaran Najeriya A Safiyar Litinin


Maharba da Kayan Yakinsu.
Maharba da Kayan Yakinsu.

Wata mata ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a kasuwar Jagwal, inda ake sayar da wayoyin hannu a garin Azare dake Jihar Bauchi, ta kashe mutane akalla 12.

Wani mazaunin garin Azare yayi mana Karin bayani…yayin da wata mace dake dab da wurin da abin ya faru ma ta yi mana Karin haske kan wannan lamarin…

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin na Azare, amma kuma a can baya, kungiyar Boko Haram ta kai ire-iren wannan harin a nan Azare, inda a cikin ‘yan kwanakin nan aka kai har sau uku.

Tun da fari a jiya lahadi, rundunar sojojin Najeriya ta ce ta fatattaki ‘yan Boko Haram daga garin Chibok na Jihar Borno, inda a watan Afrilu tsageran kungiyar suka sace dalibai mata fiye da 200.

Jami’an sojan Najeriya sun ce sojoji sun kwato garin na Chibok da maraicen asabar, kwanaki biyu bayan da ‘yan Boko Haram suka kwace shi.

Mazauna garin sun ce ‘yan kato da gora da kuma mafarauta sun taimakawa sojojin wajen kwato Chibok.

A yayin da ake cikin wannan ne kuma gwamnatin Jihar Adamawa ta ce ita ma zata karfafa guiwar kafa kungiyoyin ‘yan kato da gora a garuruwan jihar, kamar yadda aka yi a jihar Borno, domin kare garuruwan daga ‘yan ta’adda. Mr. PP Elisha shi ne kakakin gwamnan na Adamawa..

A halin da ake ciki, wani shugaba na maharban da suka kwato Maiha da Mubi daga hannun ‘yan Boko Haram, yay aba da taimakon da gwamnatin jihar Adamawa ta ba su, amma yace jihohin arewa ne ya kamata su hada kai su taimaka domin a kawar da ‘yan bindiga.

An dai ci gaba da addu’ar Allah Ya karya lagon wadanda suke kawo wannan fitina a arewa…

Labaran Najeriya Da Dumi-Duminsu - 4'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG