Kamfanin na'urorin zamani na Amurka, Apple, ya fitar da wasu sabbin nau'in wayarsa mai farin jini ta iPhone har guda biyu, wadanda aka kara musu fadin fuska da kuma sauri.
A yau talata kamfanin na Apple ya bayyanawa duniya sabbin wayoyin na "iPhone 6" da "iPhone 6 Plus" wadanda shugaban kamfanin Tim Cook, ya bayyana su a zaman ci gaba mafi girma da muhimmanci da aka samu ga nau'in wannan waya ta iPhone da aka fara sayarwa a fadin duniya a shekarar 2007.
Har yanzu kamfanin Samsung na kasar Koriya ta Kudu shi ne kan gaba a duniya wajen sayar da wayoyi, fiye da kamfanin Apple nesa ba kusa ba. Amma kamfanin na Amurka yana cikin wadanda suka fi daraja a duniya.
Kamfanin Apple yace farashin iPhone 6 wanda shi ne karami mai tsawon santimita 12, zai fara daga Dalar Amurka 199. Daya wayar, iPhone 6 Plus mai tsawon santimita 14, farashinta zai fara daga Dala 299.
Za a fara sayar da su ranar 19 ga watan Satumba.
Haka kuma kamfanin Apple ya shirya fito da wata sabuwar na'ura mai kamar agogo da za a rika daurawa a hannu, mai suna iWatch, wadda zata iya taimakawa jama'a wajen sanya ido kan lafiyar jikinsu, da yin saye-saye, da kuma lura da tsaron gidajensu daga ko ina suke a duniya.