Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likitan Da Yayi Jinyar Mai Ebola A Lagos Shi Ma Ya Kamu da Cutar


Ma'aikatan lafiya a Saliyo su na binne wani wanda cutar Ebola ta kashe

Najeriya ta ce likitan da yayi jinyar mutum na farko da cutar Ebola ta kashe a Lagos kwanaki goma da suka shige, shi ma ya kamu da wannan cuta da ba ta da magani.

Ministan kiwon lafiya na Najeriya, Onyebuchi Chukwu, ya fada yau litinin cewa an killace wasu mutanen su 8, yayin da ake jiran sakamakon gwajin da aka yi ma wasu mutane 3 a kokarin da hukumomi suke yi na hana bazuwar wannan kwayar cuta mai kisa.

A halin da ake ciki, Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Amurka zata tura kwararru kan kiwon lafiyar jama'a su 50 zuwa Guinea da Saliyo da kuma Liberiya, inda cutar Ebola ta kashe mutane fiye da 800 a wannan shekara.

A makon da ya shige, hukumar kiwon lafiya ta Duniya ta bayyana wani shirin gaggawa na Dala miliyan 100 tare da kasashen uku da abin ya shafa domin karfafa ayyukan dakilewa da kula da masu cutar. Wani kakakin hukumar yace za a bukaci kwararru 600 domin aiwatar da wannan shirin.

XS
SM
MD
LG