Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Kunar Bakin Wake Ta Kashe Kanta Da Wasu Mutane 5


Kwamishinan 'yan sanda na kano, Aderenle Shinaba da ‘yan sanda a wurin da bom ya fashe a Kano, 24 ga Yuni 2014.

Mutane akalla 5 ne suka mutu tare da wata macen da ta kai harin kunar bakin wake yau litinin a gidan mai na NNPC Mega Station dake unguwar Hotoro, kan hanyar zuwa Maiduguri a Kano.

Shaidu na gani da ido sun ce wannan matar ta tayar da bam din dake boye a jikinta a lokacin da ta doshi inda mutane suke sayen kananzir. 'Yar kunar bakin waken ta tarwatsa kanta nesa da inda mutane suka fi yawa a wannan wuri, ganin yadda a yanzu ba a kyale mutane da yawa su na taruwa a bakin inda ake sayar da man a lokaci guda.

Wannan shi en bam na uku da ya tashi a Kano cikin kasa da sa'o'i 24, Akwai rahotannin cewar wata matar ma ta yi kokarin kai harin kunar bakin wake a dab da kantin ShopRite, amma an ce ita kadanta ta mutu.

Ga rahoton da Mahmud Kwari ya aiko mana daga Kano.

XS
SM
MD
LG