Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juventus Ta Nada Massimiliano Allegri A Zaman Sabon Kwach Nata


Tsohon kwach na AC Milan, Massimiliano Allegri, wanda ya zamo kwach na Juventus yau laraba 16 Yuli 2014
Tsohon kwach na AC Milan, Massimiliano Allegri, wanda ya zamo kwach na Juventus yau laraba 16 Yuli 2014

A yau laraba, kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta nada Massimiliano Allegri a zaman kwach nata domin maye gurbin Antonio Conte wanda haka kwatsam jiya talata ya ajiye wannan kujera.

A watan janairu kungiyar AC Milan ta kori Allegri a matsayin kwach nata bayan shekaru 3 da rabi, inda har a shekararsa ta farko ya jagoranci kungiyar ta lashe wasannin lig-lig na Italiya.

Shi kuwa Conte, shekaru 3 ke nan a jere yana jagorancin Juventus tana lashe wasannin lig-lig din, amma jiya talata ba zato ba tsammani sai yace ya gaji, kuma kalamunsa sun nuna alamun cewa ya watsar da aikin ne a saboda sabanin dake tsakaninsa da jami’an Juventus kan irin ‘yan wasan da zasu saya a bana. An ce ya so su sayi ‘yan wasa masu tsada kamar Alexis Sanchez na Chile, wanda ya bar Barcelona ya koma Arsenal, da kuma Juan Cuadrado na Colombia.

A maimakon haka, sai manyan Juventus suka shiga zawarcin ‘yan wasa kamar Patrice Evra na Manchester United, da Alvaro Morata na Real Madrid da kuma Juan Manuel Iturbe na Hellas Verona.

An yi ta ambaton sunan Allegri a zaman wanda watakila zai gaji Cesare Prandelli a zaman kwach na kungiyar kwallon kafar Italiya, amma a yanzu ana ganin cewa Conte da kuma Roberto Mancini sune kan gaba.

XS
SM
MD
LG