Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamuyi Kokari Muga mun Samu Canji Amma Canji Bazai Yuba Sai Anyi Zabe


Matasa a Najeriya
Matasa a Najeriya

A duk lokacin da zabe ya karato a Najeriya, abun tsoro shine matasa, domin yadda ake amfani dasu wajen bangar siyasa, lamarin dake jawo tashin hakali a wasu lokuta.

Sai dai a wannan karon matasa a jihar Taraba, dake arewa maso gabashin Najeriya, sun yunkuro inda yanzu haka daya daga cikin su ne shugaban jamiyyar, NCP, a jihar.

Shugaban jam’iyyar, ta NCP, komrade Abdullahi Bello, yace “ Don ni matashi ne yasa na dawo kan matasa kafin inyi maganar abunda ya tsayar dani, a duk kungiyoyin siyasa na jihar Taraba, nine kawai matashi, da yake shugaban kungiyar siyasa, shi yasa idan muka je inda matasa suke sai ace kai ka tashi kayi Magana, toh, matasa mu gode mun fara nisa a siyasa, insha Allahu zamuyi iya kokarinmu muga mun samu canji, amma canji bazai yuba sai anyi zabe, kada ka yarda kayi barci zai kasan kana da katin zabe.”

Matasa Taraba -3'17"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG