Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Ci Zarafin 'Yan Sanda A Bakin Aiki


An gurfanar da wasu matasa ukku, a kotu, a dalilin cin zarafin wani mai ‘yan Sanda, a garin Ado Ekiti, dake jihar Ekiti.

Wadanda aka gurfanar sune Tope Muhammad,mai shekaru talatin da bakwai (37) Obinna Bassey, mai shekaru (27) da na ukku Kingsley Igwe.

Matasan sun ci zarafin Sufeton ‘yan Sanda Adefemi Oguntade da Saja Ebrudge Odunayo, a lokacin da suke gudanar da aikin su na ‘yan Sanda ne a birnin Ado Ekiti.

Laifin da wadannan matasa suka aikata ya sabawa sashe na 356 sakin layi na 1 da na 3, na kundin laifuffukan jihar Ekiti.

Mai shara’a Adesoji Adegboye, ya bada balin wadanda ake zargin kuma y adage shara’a zuwa 28, ga watan Oktoba.

XS
SM
MD
LG