Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Yaron Mota Ya Gan-Gantsarawa Fasinja Cizo


Wata kotun majistire dake Ikeja, ta kama wani matashi mai sana’ar yaron mota ko kwandasta, dan shekaru 25 da haihuwa mai suna Tobi Ogunremi, bisa zargin sa da gantsarawa wani fasinja cizo.

Matashin wanda ke da zama a gida mai lamba 5, kan layin Idi-Orogbo, na fuskantar aikata laifin cin zarafi.

A cewar sufetan ‘yan sanda Victor Eruada, wanda ake zargin ya aikata laifinne ranar 7 ga watan Disambar da muke ciki a dai-dai kan mahadar da ake kira Shyllon Junctio, da ke Illupeju a jihar Legas.

Matashin ya bayyana cewa fasinjanne ya hana shi sauran canjin kudin mota da ya kamata ya biya shi kana daga karshe ya watsar masa ta su a kasa. Jami’in ya bayyana cewa kara da cewa Adedayo, ya sami raunika a bakinsa biyo bayan naushin da yaron motar ya yi masa a lokacin da suke gardama.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa kotun ta bada belin matashin a kan kudi Naira dubu ashirin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG