Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TAMBAYA: Wadanne Irin Ayyukan Gida Suka Kamata Ka Sa Hannu?


Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, shirin samartaka na dandalinvoa kan tattauna da matasa maza da mata domin jin ra’ayoyi daban daban musamman a kan batutuwan da suka shafi soyayya, zamantakewa da kuma al’amurran yau da kullum.

Ta dalilin haka ne a wannan karon muke so muji ra’a yoyinku akan ko ya kamata mai gida ya rika taya matarsa gudanar da wasu ayyukan gida, kuma wadanne irin ayyukan ya kamata ya taimakawa uwargidansa da su?

Muna bukatar ra’ayoyin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG