Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon dan Wasan Tottenham ba zai Samu Wasa a karawar su da Liverpool ba


Tsohon fittaccen dan wasannan na kungiyar kwallon kafar Tottenham, ba zai samu tafiya da sauran abokan wasan kungiyarshiba, A karawa da zasuyi da ‘yan kungiyar Liverpool.

Shi dai Gareth Bale ya ji rauni a kunkurunshi, wanda shi zeyi sanadiyyar da ba zaibi abokan kungiyar shi ta Real Madrid zuwa Liverpool a gasar wasan League na UEFA ba.

Shi dai Bale ya samu jimuwar ne a tsokar saman kafarshi ta dama, a lokacin da yake wani wasan kasa-da-kasa a satin da ya wuce.

A baya dai ya kalli wasan yan kungiyar shi ta Real Madrid inda ta ci 5 su kuma yan wasan Levante suka tashi da 0 a ranar Asabar lokacin yana kan benci. Kamin kungiyar zakarun kasashen turai ta bayyanar da dacewar gwagwarmayarshi a ranar litinin.

Yanzu dai a hukumance an fitar dashi, bayan gazawa da yayi na tsayayun mutane 20 na tawaga don zuwa filin wasa na Anfield. Ko da yake dan wasannan Karim Benzema ya girgiza kafarshi me raunin don ganin an sa sunanshi a ciki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG