Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sridevi Da Mijinta Sun Yi Nasara A Kotu


Sridevi
Sridevi

Fim din wanted da ya fito da bajintar Salman Khan a shekara 2009, ya samu tsaiko a lokaci da aka yi kokarin fito da kashi na biyu na fim din, saboda a wancan lokacin an zargi Boney Kapoor da matarsa Sridevi mai yin fina finai da Salman Khan, da laifin satar fasaha.

Amma yau bayan da aka kwashe shekaru bakwai ana ta kai ruwa rana koto ta wanke su kuma daga duk wamni zargi, saboda haka suna iya ci gaba da fim din na “Wanted 2”.

Rahotan na nuni da cewa Birbal Singh, wanda ya kaisu kotu ya nemi Boney Kapoor, da ya bashi kudade fiye da dalar Amurka dubu dari ($100,000) wanda hakan shine ake zaton cewa yayi dalkilin zuwa kotu da batun satar fasaha.

Wannan batun na neman zaman ruwan dare a kasar indiya inda ake samun mutane marasa kirki na bukatar magudan kudade daga jarumai ko kuma su bata masu suna.

Da aka tabayeshi ko jinkirin kotu ya kawo masa tsaiko a harkarsa na fina finai sai yace ko kadan a’I mutun baya barin irin wadanna abubuwa su zame masa cikas amma yace sai zama da kamar wuya ace ayi fim din Wanted 2, batare da jarumi Salman Khan ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

XS
SM
MD
LG