Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya sun Takawa 'Yan Boko Haram Birki


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Hedkwatar tsaron rundunar Sojojin Najeriya, dake babban birnin tarayya Abuja, tace ta samu nasarar kauda hare-haren, da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai Maiduguri da Kwanduga, sun kuma kwace makamai da motoci daga hannun su.

Babban daraktan hulda da jama’a, na rundunar Sojojin Najeriya, Janar Olukolade ne ya sanarda haka a wata takarda sanarwa da ya aikewa manema labarai, yace rundunar ta samu nasarar fatattakar ‘yan kungiyar ta Boko Haram, a wani yunkuri da suka yi har sau biyu na shiga birnin Maduguri da Kwaduga, amma Sojojin Najeriya suka taka masu birki.

Yace yanzo kuma suna kokarin ganin cewa sun fatattaki ‘yan kungiyar ta Boko Haram, daga garin Munguno, yana mai cewa sun kashe wadannan ‘yan kungiyar da dama sakamakon arangamar da suka yi dasu, kuma ana bincike gano inda sauran ‘yan kungiyar suke.

Janar Kolade, ya kara da cewa sun gano wasu kayayyaki da dama harda wasu motoci uku dake dauke da abubuwan fashewa da kuma wata motar yaki ta Sojoji da bindigogi da harsasai da dama, sun kuma kama wasu 'yan kungiyar ta Boko Haram da ransu.

Boko Haram - 2'49"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG