Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Marabci Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok


Yau ne shugaba Muhammadau Buhari na Najeriya a gidan gwamnati ya karbi ziyarar Amina Ali, daya daga cikin dalibai ‘yan mata sama da 200 na makarantar Chibok da ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka sace, ta isa fadar shuganaban kasar ne tare da iyayenta da gwamnan jahar Borno, da ministan tsaro na kasa da sauran hafsoshin soji wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajan yaki da ‘yan kungiyar a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Bayan da aka kammala ganawar Malam Garba Shehu, kakakin shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati ya yi wa wakilin sashen Hausa Umar Farouk Musa Karin haske akan yadda ganawar shugaban kasar ta kasance da maziyartan nasa. Kakakin ya kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi juyayi da takaicin irin abin da ya faru da wannan yarinya.

Kakakin ya kara da cewa shugaban ya nuna karfin hali domin kuwa har jaririn da take tare da shi ya dauka ya rike a hannun sa, ya zauna ya jajanta masu, ya jajanta wa kasa, sa’annan yace yana murna da fitowar ta a raye, kuma y ace yana jin takaici a zuciyar sa.

Daga karshe ya bayyana cewa shugaban ya bayyana cewa duk irin taimakon da kasa zata iya yi wa wani dan kasa to babu shakka za’a yiwa wannan yarinya, kuma likitoci sun fara duba ta domin tabbatar da lafiyar ta dakuma taimakawa rayuwar ta daga lalacewa.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG