Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Firimiya Da Laliga 2016/17 Mako Na 36


A wasannin da aka fafata a bangaren Firimiya lig na kasar Ingila 2016/17 mako na 36 a ranar Jumma'a da ta gabata 5/5/2017 kungiyar kwallon kafa ta Westham, ta doke Tottenham daci 1-0. A ranar Asabar kuwa Manchester City ta lallasa Crystal palace da kwallaye 5-0, Hull City ta sha kashi a hannun Sunderland da kwallo 2-0, Leicester city ta doke Watford da kwallaye 3-0, Bournemouth ta yi canjaras 2-2 tsakaninta da Westbromwich, Swansea City 1-0 Everton.
A jiya lahadi 7/5/2017 Liverpool ta yi canjaras 0-0 da Southampton, Arsenal ta samu nasara a kan Manchester United, da kwallaye 2-0.

A yau kuma za'a kara tsakanin kungiyar Chelsea, da Middlesbrough's da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya da Nijar.

Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ke Jan ragamar teburin da maki 81 sai Tottenham, ke biye da su a mataki na biyu da maki 77 Liverpool, tana mataki na ukku da maki 70.

A kasan teburin kuwa Hull City, tana mataki na goma sha takwas da maki 34
Middlesbrough's tana mataki na goma sha tara da maki 28, Sunderland na kasan teburin a mataki na 20 da maki 24. A bangaren Laliga na kasar Spain 2016/17 shima mako na 36, Ranar Jumma'a Sevilla, ta yi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Real Sociedad.

Ranar Asabar da ta gabata Sporting Gijon ta yi nasara akan Las Palmas 1-0
Atletico Madrid ta doke Eibar daci 1-0, Barcelona ta lallasa Villarreal, da kwallaye 4-1 Granada ta sha kashi a hannun Real Madrid, da kwallaye 4-0. A jiya lahadi Alaves 1-0 Athletic Bilbao, Valencia ta doke Osasuna da kwallaye 4-1 Deportivo 1-2 Espanyol Malaga ta doke Celta Vigo daci 3-0.

Yau kuma za'a gwabza tsakanin Leganes da Real Betis da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar da kamaru, Barcelona tana mataki na daya asaman teburin da maki 84 Real Madrid, tana bayanta a mataki na biyu da maki 84, Atletico Madrid, tana mataki na ukku ita kuma da maki 74.

Kasan teburin Sporting Gijon a matsayi na goma sha takwas da maki 27
Granada a matsayi na goma sha tara da maki 20 sai Osasuna a mataki na ashirin da maki 19.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG