Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Tsarin Hukumar Makarantun Jihar Califonia.


Daliban Makaranta a Amurka
Daliban Makaranta a Amurka

Shuwagabannin makarantu na karamar hukumar Los Alamitons ta jahar Kalifoniya a nan Amurika. sun cinma matsaya cewar iyayen yana na iya biyan $100 kwatan kacin naira =N=17,000 don kada a bama ‘yayansu aikin gida na sati daya.

Hukumar makarantu ta wannan karamar hukumar sun aika ma iyayen ‘yara da takardu zuwa gidajensu dan gane da wannan tsarin, cewar idan har iyaye basu so ‘yayansu suyi aikin gida har na tsawon sati daya to zasu biya wadannan adadin kudin. Shidai wannan tsarin da suka kirashi da suna Project Leap a turance wata hanya ce da za’aiya samar da kudade don gyaran ajujuwa. Amma ana ganin kamar wannan gwajin bazai je ko in aba. Wannan wani abun takaici ne kuma hanyace da za’abama yara cin hanci, acewar wata mazauniya yankin kuma uwar wasu yara.

Ta kara da cewar, bata jima danta dadiba don har yafara cemata MAMA ko zasu gwada ne? Sai tace bazata bar wani malami ko makaranta su lalatamata yaro ba, su koyamishi abun da bai dace ba. Wannan ba dabi’a me kyau bace kace na bada $ 100 don kada yaro na yayi abun da zai amfaneshi agaba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG