Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Roma Da Villarreal Zasu Fafata A Europa League 2016/17 Last 32


A cigaba da wasannin cin kofin zakarun nahiyar Turai da akeyi a matakin zagaye na goma sha shida, jiya Kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta doke Leicester city daci 2-1.

FC Porto, ta sha kashi a gidanta a hannun Juventus, da kwallaye 2-0, za'a sake karawa ta biyu a tsakanin Kungiyoyin ranar Talata 14/3/2017.

A gasar cin kofi na Europa League 2016/2017, a matakin zagaye na 32 karawa ta biyu, jiya laraba Manchester United, ta yi waje rod da Saint Etienne, da kwallo 1-0, inda a haduwarsu ta farko Manchester, ta sha 3-0, Ita kuwa Schalke, 04, tayi kunnen doki a gidanta tsakaninta da Paok, sai dai Schalke, ta samu zuwa zagayen gaba Sakamakon karawar farko ta sha 3-0.

Itama Fenerbahce, tayi canjaras 1-1 da Krasnodar, a jiya inda akarawar farko a ka doke Fenerbahce 1-0, Sakamakon haka Krasnodar, ta samu zuwa zagaye na goma sha shida.

A yau kuma za'a cigaba da fafatawa a sauran wasannin inda kungiyar Besiktas zata kara da Hapoel Be'er Sheva

Roma da Villarreal, Zenit da Anderlecht, sai Copenhagen da Ludo Razgd, Akwai Florentino da Borussia Monchenglabach. Sauran sune Shakhter D zasu karbi bakuncin Celta Vigo, Genk da Astra Giurggiu, Lyon zata fafata da AZ Alkmaar, Osmanlispo da Olympiakos, Ajax zata kara da Legia Warsaw, Sai Sparta Praha su barje gumi da FC Rostov, Apoel zata gwabza da Athletic Bilbao.

Za'a buga wasanninne a lokuta daban daban agogon Najeriya, Nijar da kamaru tun daga misalin karfe biyar na yammaci har zuwa karfe tara na dare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG