Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Zata Gwabza Da Juventus A Wasan Karshe Na (UCL)


A jiya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta samu kaiwa ga wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai Uefa champions league, na shekarar 2016/17

Kungiyar Real Madrid, ta samu wannan nasaranne sakamakon wasan da sukayi na dab da na karshe tsakaninta da Atletico Madrid, inda a karawarsu ta farko a satin da ya wuce, Real Madrid, ta lallasa Atletico Madrid, da kwallaye 3-0 sai kuma jiya Atletico ta samu nasara akan Real Madrid, da kwallo 2-1

Wannan yaba kungiyar ta Real Madrid, jimillar kwallaye 4 ita kuwa Atletico tana da 2. Don haka Real Madrid zata kece raini a wasan karshe tsakainta da Juventus, ranar Asabar 3 ga watan yuni 2017 a filin wasa na Cadiff dake Wales.

Wayadanan kungiyoyi biyu sun taba haduwa sau 13 tun bayan haifuwarsu Juventus, tayi nasara akan Madrid, sau 6. Ita kuma Real Madrid, sau 5 anyi kunnen doki sau 2.

A bangaren gasar cin kofin Turai kuwa Europa league 2016/17 a matakin wasan kusa da na karshe zagaye na biyu, a yau Manchester united, zata karbi bakuncin Celta Vigo.

A karawar da sukayi ta farko Manchester, ta doke Celta da kwallo 1-0 haka kuma Lyon, zata Kara da Ajax, a zagaye na biyu,a haduwarsu ta farko Ajax ta lallasa Lyon, da kwallaye 4-1

Za'a buga wasanne da misalin karfe takwas da minti biyar na dare agogon Najeriya Nijar kamaru da Kasar Chadi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG