Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Lashe Gasar La-Liga A Karo Na 33


Zinedine Zidane
Zinedine Zidane

A jiya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasarar lashe gasar laliga na 2016/17 na Kasar Spain da maki 93 a wasanni 38 da aka buga Madrid ta doke Malaga da kwallo 2-0, a gidan Malaga a wasan karshe a jiya lahadi 21/5/2017.

Kungiyar Real Madrid, ta shekara Hudu rabonta da ta dauki wannan Kofi sai dai itace kungiyar da tafi kowace kungiya a kasar daukan wannan Kofi domin ta samu nasarar daukan kofin sau talatin da ukku

Ita kuwa abokiyar hamayyanta Barcelona ita ce tayi na biyu da maki 90, inda ta jera shekaru tana lashe gasar kuma itace kungiya ta biyu wajan lashe kofin inda ta lashe sau ashirin da hudu

Atletico Madrid ke biye a mataki na uku da maki 78 Itama ta lashe wannan Kofi sau Goma kuma itace ta Uku a daukan kofin, Sevilla ta na mataki na Hudu da maki 72.

A kasan teburin kuwa Sporting Gijon, na mataki na Sha takwas da maki 31, Osasuna a mataki na sha tara da maki 22 sai Granada a mataki na ashirin da maki 20.

XS
SM
MD
LG