Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya na Harsashen Kashe Naira Miliyan Zambar a Shekara Mai Zuwa


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Ministan kudi, kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala, ta gabatar da kasafin kudin badi ga Majalisar kasa.

A wannan kasafin kudin dai Gwamnati tayi harsashen kashe Naira miliyan zambar hudu da miliyan dubu dari uku.

A bayanin da ta yiwa manema labarai, Ngozi Okonjo Iweala, tace Gwamnati, na kara bude idanunta ne, ga zahirin dake tafe domin tana shirin hako gangar mai miliya biyu da digo biyu ne kullum.

Kuma da fatan cike gibin kasafin kudin ne daga kudaden shigan da za’a samu daga wasu bangarori da bana mai ba, Ngozi ta kara da cewa mun rage bunkasar tattalin arzikin kasar daga kashi shida da digo uku cikin dari, zuwa kashi biyar da digo biyar cikin dari, kuma shine ma’aunin tattalin arzikin, mafi aminci a duniya.

Kasafin kudin Najeriya - 3'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

XS
SM
MD
LG