Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Kasar Japan Biyu Sun yi Murabus


Biyu daga cikin ministoci mata biyar a gwamnatin Prime Minista, Shinzo Abe na kasar Japan sunyi murabus
Yau litini matan biyu suka yi murabus bisa zargin cewa sunyi almubazaranci da kudin jama'a domin samun kuri'u.
A makon jiya zargin da aka yiwa Ministar harkokin cinnikayya Yuko Obuchi yar tsohon Prime Ministan kasar, ya fara kunko kai, akan cewa ta kashe dubban daloli, na kudin zabe domin yiwa sayen tikitin shiga sinima da wasu kayayyaki rangwame a mazabarta.
Yan sa'o'i kafin ita Yuko Obuchi tayi muraus, Ministar shari'a Midori Matsushima itama ta yi murabus bisa zargin cewa ta keta ka'idar dokar zabe a lokacinda ta rarrabawa masu kaunar ta takardun dake da suke dauke da hoton ta, wa wasu masu jefa kuri'a mazabarta.
Yau Litinin Prime Ministan Japan Shino Abe yace shine ya nada su, a saboda haka shine keda alhakin duk wani abinda ya faru. Ya nemi gafarar yan kasar sa kuma yace zai nada wadanda zasu maye gurbinsu.

XS
SM
MD
LG