Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United ina aka sa Gaba?


Manchester United
Manchester United

Kamar yadda Louis Van Gaal yake fadi a kowanne lokaci wato lamari sai ya ‘baci kafin ya zama nagari a Manchester united.

Ban taba tsammanin lamarin zai yi wannan lalacewar ba.

Kusan wata biyu da suka shude, Louis ya yunkura daga kujerarsa domin tafawa da dan wasansa na Netherlands wajen nuna murnarsa a filin wasan inda su Netherlands suka fatattaki abokan karawarsu 5-1 wato spain a wasan cin kofin kwallon duniya da’a kayi a Brazil in ba’a manta ba.

Idan aka kwatanta da yanzu, in da shi Louis din ya manne a kujerar sa a lokacin wasan na su Manchester united inda aka ragargazasu da 4-0.

A gefen hannun dama wanda ke zaune shine ne Ryan Giggs mataimakin Koch Louis Vaan Gaal wanda ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa.

Bayan biyo rashin sa’ar ci wasa a farkon da aka fara na premier league, damuwa tafara karuwa kasancewar rashin samun cin wasa kodaya, damuwar tasa ana tunanin ko yanda shi Koch dinne yake shirya tsarin wasansa ne baiyiba? Shidai Koch din yana amfani da wani tsari da ake kira 3-5-2, kuma yana bukatar dan wasan baya mai kyau.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:45 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG