WASHINGTON DC —
Malaman makaranta ‘yan kwantragi bangaren kananan makarantu,a jamhuriyar Nijar, sun koka kan yadda har yanzu gwamnati bata biya su albashin su ba, wanda a cewar su rashin sa hannu ne ya kawo tsaikon.
Magatakarda na kungiyar, Malaman makaranta ‘yan kwantragi, Yau Abdu, yace wata biyu Kenan ba a biya Malaman makaranta ba saboda haka idan har gwamnati na bukatar a koma bakin aiki ba tare da tashin tashina ba toh ta gaggauta biya albashin.
Duk lokacin da matsala ta taso ana zama a tattauna tsakanin Malaman makarantar da mahukunta kuma ana samun fahimta a baya.
Malaman makarantar sun yi kira ga shuwagabanin dasu dauki maganarsu da mahimmaci gani cewa gwamnati a can baya tayi alkawarin daukar batun ilimi da mahimmanci.
Facebook Forum