Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya na Jagoranci Wajen Yaki da Cutar Ebola a Yammacin Afirka.


Hukumomin Majalisar dinkin duniya da kiwon Lafiya na duniya
Hukumomin Majalisar dinkin duniya da kiwon Lafiya na duniya

Sakatare-Janar na Majalisar dinkin duniya, Banki Moon, ya ce Majalisar, na jagoranci wajen yaki da barkewar cutar Ebola a Yammacin Afirka.

Ya gaya wa manema labarai jiya Talata cewa da shi da Shugabar Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Margaret Chan, za su fito da jadawalin kasa da kasa na yaki da cutar a gobe Alhamus, a wurin taron gaggawa na Kwamitin Sulhun Majalisar, dinkin duniya.

A wannan ranar ake kuma sa ran Kwamitin zai kada kuri'a kan kan daftarin da Amurka ta gabatar na kiran kasashe su gaggauta aikawa da kayan tallafi, asibitocin wuccin gadi da ma'aikatan jinya zuwa kasashen da cutar ta shafa, sannan kuma a dage dokar hana tafiya irin wadannan wuraren.

Mr. Ban ya ce babban zauren Majalisar, zai yi wani muhimmin taro kan wannan al'amarin a mako mai zuwa. Ya bayyana barkewar Ebolar da cewa wani tashin hankali ne mai saurin muni da kuma ke bukatar daukar mataki cikin sauri.

Jiya Talta Shugaban Amurka Barack Obama ya ba da sanarwar tura dubban sojojin Amurka zuwa Yammacin Afirkar don su taimaka a harkokin lafiya, inda mutane kusan 2,500 su ka mutu sanadiyyar barkewar wannan cutar.

XS
SM
MD
LG