Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maharan Boko Haram Na Kokarin Shiga Garin Maiduguri Amma Sojoji da JTF Sun Hanasu.


Tun a daren jiya zuwa wayewar garin yau ne mazauna garin Maiduguri suke jin ‘karan harbe-harbe da karan wasu ababuwa masu fashewa. Hakan dai ya haifar da fargaba da zulumi ga zukatan jama’a, zuwa wayewar garin yau ne dai jama’a dake baki bakin gari suka rika ficewa daga unguwannin nasu don shiga cikin gari domin gujewa abinda ka iya faruwa.

Wakilinmu Haruna Dauda ya fita kan babban titin dake cikin garin Maiduguri, inda ya ganewa idon sa daruruwan ababan hawa nata shiga cikin gari, sai kuma mata da kananan yara nata takawa da kafafunsu don gudun tsira daga wannan hari da ake tsammanin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suke kokarin kawowa zuwa birnin Maiduguri.

Wata Majiya ta shaidawa wakilin namu cewa wadannan mahara nata arangama ne da ‘yan kungiyar sa kai na civilian JTF, da hadin gwaiwar jami’an tsaron sojan kasar, wanda ake ta misayar wuta da mutanen da ake tsammanin ‘yan ‘yan kungiyar Boko Haram din ne.

Wakilinmu ya kira wasu dake cikin ‘yan kungiyar civilian JTF, wanda suka shaida masa cewar suna filin daga, kuma daga jin yadda abubuwa ke gudana ta wayar tarhon za’a san cewar ana ta barin wutane tsakanin su da wadannan mahara. Maharan dai nason shiga cikin garin Maiduguri tun jiya amma ‘yan kungiyar JTF sukayi musu birki.

Cigaba da wannan hari dai yazone dai dai lokacin da shugaban Goodluck Ebele Jonathan, yazo garin Maidugurin don gabatar da yakin neman zaben sa, inda a nan nema yayi alkawarin kawo karshen wadannan ‘yan’yan kungiyar, dayace nan ba da dadewa ba zai kawo karshensu.

Yanzu haka bayanai da muke samu daga karamar hukumar Monguno dake jihar Borno, wadda take karamar hukuma daya daga cikin kananan goma dake arewacin Bornon da ‘yan bindigar basu mamaye ba dakuma ke da barikin soja, yanzu haka dai wadannan mahara na ta fafatawane da jami’an sojan garin, sai dai wasu bayanai na nunin cewar maharan ne ke da iko a wannan garin, yayin da wasu ke cewa jami’an sojan haryanzu suke da wannan gari, har yanzu dai babu wani takamaiman bayani daga hukumomin tsaron kasar.

Sai dai wata sanarwa da mataimakin direktan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri, Kanal Sani Usman ya aikewa manema labarai wanda ya bada sanarwar haramta zirga-zirga har na tsawon awanni ashirin da hudu kuma illa masha Allah. Yanzu haka dai jiragen yaki na cigaba da shawagi a sararin samaniya domin gano inda wadannan hakara suke. Wasu bayanai daga gurin jama’a na cewa sojojin dake tsaron mashigar garin Maidugurin dai sun arce alokacin da maharan suka tunkaresu, amma maharan basuji da dadi ba a matasan ‘yan kungiyar JTF.

XS
SM
MD
LG