Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kano Pillars Ta Yi Babban Rashin Dan-Wasan Tsakiya


Chinedu Udoji
Chinedu Udoji

Kungiyar kwallon kafar Kano Pillars, ta bayyana alhininta na rashin dan wasanta na tsakiya Chinedu Udoji, wanda ya rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da shi a daren jiya.

Shugaban tsare-tsare na kungiyar Alh. Faruk Haladu, ya fitar da wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun kungiyar Idiri Rilwanu Malikawa, inda ya bayyana dan wasa Udoji, a matsayin dan wasa mai kwazo.

Haladu, ya bayyana cewar dan wasan ya rasu a wani hadari da ya same shi akan titin Independent Road, a unguwar Bamfai cikin birnin Kano. Rahotannin sun tabbatar da cewar dan wasan yana kan hanyar sa ta zuwa gidan sa ne dake rukunin gidajen Badawa.

Matashin dan wasan ya kai ziyara ga tsohuwar kungiyar sa ta Enyimba FC, biyo bayan wasannin su na mako 6, da suka tashi kunnen doki 1-1 da abokan karawar su a jiya Lahadi.

Dan wasan na cikin mota mai dauke da lamba KSF 499 BF. Gawar margayin Udoji, tana dakin ajiye gawarwaki na Asibitin kwararru na Murtala Muhammad, dake cikin birnin Kano.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG