Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Sun Kosa da Najeriya Kan Kwallon Kafa.


Acikin wani abin takaici kan kallon kafar Najeriya, da alama dai kwallon kafar Najeriya dai na cikin tsaka mai wuya.

Duk dayake dai kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagle har yanzu nada damar samun guri a wasan share fage na gasar cin kofin nahiyar Afirka (Africa Cup of Nation) domin kare matsayin kasar na zakaran wasa, duk da yake dai basu fara wasan wannan shekara ba da wani abin azo agani.

Ranar Asabar ne shugaban CAF Issa Hayatou yake gayawa ministan wasanni na Najeriya Tammy Danagogo cewar duniya fa ta kosa da Najeriya a bangagaren kwallon kafa. Inda yace, “Na roƙi shugaban hukumar ƙwallon ƙafa FIFA Sepp Blatter kada ya dauki mataki kan Najeriya ranar Juma’a, saboda ‘yan wasan kasar na mata na rukunin karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka kuma dakatar da kasar zai iya gurguntar da ita ga abokan karawa da kuma masu tallafawa wasan. Mun kuma ji bayan sakamakon kotu cewa duniya ta kosa da Najeriya, kuma gaskiyane.”

Da alamar ana kokarin sa miliyoyin ‘yan wasa masu tasowa cikin hatsaril, wasu kuma wa’yanda ke jin babu abinda zai shafesu indan har FIFA ta kori kasar Najeriya ko ta dakatar dasu, idan kuma har takai ga wannan halin hukumar wasan ta dakatar da Najeriya to fa baza’a samu damar sauraron maganar ba a taron daza’ayi na watan 29 ga watan Mayu shekara ta 2015. Kuma zai zama abi mafi muni ga kwallon kafar Najeriya.

XS
SM
MD
LG