Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Ingila Ta Sha Kashi A Hannun Jamus


A cigaba da wasannin da akeyi na sada zumunci tsakanin kasa da kasa ajiya kungiyar kwallon kafa ta Germany ta doke kasar Ingila da ci 1-0, Scotland tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Canada.Yemen 0-1 Palestine, Georgia U21 ta lallasa Iceland U21 da kwalaye 3-1.

Kasar Cyprus ta samu nasara akan Kazakhstan da ci 3-1, Greece U21 nada 2 Hungary nada 1,Philippines tayi kunnen doki 0-0 da Malaysia.

A yau kuma za a cigaba da bugawa tsakanin Kasar Kenya da Uganda, Ingila U21 da Portugal U21,sai Kasar Jordan da Hongkong, Afghanistan zata fafata da Denmark, Spain U21 da Denmark U21.

Nigeria da Kasar Senegal zasu buga wasannin ne a lokota daban daban agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

Bayan haka a yau za a cigaba da fafatawa na neman shiga gasar cin kofin duniya 2018, a yankin kudanci Amurka, inda kasar Colombia zata karbi bakuncin Bolivia.

A can yankin Asiya kuwa China da South Korea zasu kara Iraq da Australia sai Syria da Uzbekistan,Thailand da Saudi Arabia, UAE zasu fafata da Kasar Japan.

Za a buga wasannin ne a lokota daban daban agogon Najeriya da kamaru tundaga yammaci zuwa dare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

XS
SM
MD
LG