Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Facebook Ya Dauki Aniyar Yaki Da Ta'addanci


A jiya Litinin ne kamfanin Facebook, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ya rufe ko ya saka alamar tambaya ga kimanin labarai da bidiyo milliyan daya da dubu dari tara 1.9, da aka saka a shafin sa wadanda ke da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda na ISIS ko al-Qaida, cikin watanni uku na farkon wannan shekarar.

Hakan ya ninka adadin shafukan da suka rufe a cikin karshen shekarar da ta gabata. Kamfanin Facebook shine kamfanin da yafi kowanne girma a fadin duniya wajen sadarwar zamani.

Kamfanin a karon farko ya bayyana irin yunkurin da yake yi wajen bayyana kudurorin kungiyoyin ta’addanci, a yunkurin jawo hankalin kamfanoni wajen bada tasu gudunmuwa don yaki da ta’addanci a ko ina a fadin duniya.

Kungiyar kasashen Turai na matsin lamba ga kamfani na facebook, da sauran kamfanonin yada zumunta na yanar gizo, da su rika cire duk wasu bayanai da aka wallafa a shafukan su dake da alaka da ta’addanci cikin gaggawa. Ko kuma su fuskanci fushin hukumar, duk dai da cewar kamfanin na aiki tukuru wajen cimma wannan nasara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG