Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jay Jay Okocha Na Shakka Kan Kishin 'Yan Kwallon Kafar Najeriya.


Tsohon dan wasan Najeriya Jay Jay Okocha, yace yana shakka kan kishin ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya na super Eagle, alokacin da aka fitar dasu daga gasar neman cin kofin nahiyar Afirka ta shekara 2015.

Najeriya dai itace zakara mai rike da kofin wasan na nahiyar Afirka, kunnen dokin cin 2-2 kawai tayi da abokiyar karawarta ta Afirka ta Kudu. Anyi dai wasan a jihar Akwa Ibom ranar larabar data wuce, Nigeriyar dai bazata je Equatorial Guinea ba domin kare kofinta a matsayin ta na zakara mai rike da kofin nahiyar ta Afirka.

Okocha dai yana ganin cewa su kansu ‘yan wasan nada nasu laifin, bawai Koch Stephen Keshi kadai keda laifi ba. Okocha yace “ina jin maganar gaskiya itace a koda yaushe munada ‘yan wasa masu kwazo, kuma abin tambaya anan shine shin ‘yan wasan nada kishin wasan kamar da?”

Ya kara da cewa mutane na matsa musu lamba akan yakamata su nuna, suna kishin wasan, saboda wani lokaci sai kaga kamar basu damuba da sakamakon wasan.

Okocha ya kara da cewa kungiyar Eagles dai sun fara wannan wasan neman shiga bada sa’a ba, inda banda fadan neman samun tikitin zuwa karshe babu wani abu da suka sa a gaba.

Tabbas Najeriya na wani matsayi maras kyau, koda kuwa ace muna dama, “ina tunanin wani lokaci ‘yan wasa dole su shiga cikin irin wannan hali, kafin su farga suga sun dawo wasan cin kofin nahiyar Afirka. Sun dai sa kansu cikin mawuyacin hali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG