Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu ana Kyamar Masu Cutar Kanjamau.


Alamar HIV
Alamar HIV

Ana nuna wariya ga masu cutar kanjamu, cutar da ke karya garkuwar jiki.

Har yanzu dai masu cutar kanjamau, na fuskantar wariya da kyama daga al’umma. Abin ka iya kara janyo masu wasu matsalolin rayuwa.

Dandalin VOA ya zanta da wata mata da mijinta ya samata cutar mai karyar garkuwar jiki kuma daga baya suka rabu. Ita dai matar ta koka da yadda jama’a da ‘yan uwanta ke kyamarta har ma da mahaifiyarta, abinda ya sa akan dole ta koma gidan kawunta da zama wanda shi kuma bashi da karfi sosai.

Matar tayi kira da a taimaka mata da jari don ta sami abinda zata ci, ta kuma taimaka ma ‘ya’yanta.

Ga cikakkiyar hira da Baraka Bashir tayi da matar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00

XS
SM
MD
LG