Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Talata Za'a Fara Tattaunawa Akan Sako Daliban Chibok


Mai baiwa shugaban Najeriya, shawara akan hulda da jama'a Doyin Okupe, yace gobe Talata idan Allah ya kaimu za'a fara tattaunawa a kasar Chadi akan batun sako dalibai yan matan wata makaranta a Chibok arewa maso gabashin Najeriya, da yan kungiyar Boko Haram suka sace.
Doyin Okupe ya fadawa Muryar Amirka cewa bai san tawon lokacin da za'a yi ana tattaunawar ba.
Idan ba'a mance ba a ranar sha hudu ga watan Afrilu yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata maitan da saba'in daga wata makarantar sakandare a garin Chibok arewa mso gabashi Najeriya. Hamsin da biyar daga cikin 'yan matan sun samu nasarar kubucewa amma har yanzu Boko Hara na tsare da fiye da yan mata maitan.
A ranar juma'a gwamnati Najeriya, da kungiyar Boko Haram suka yi na'am da yarjejeniyar tsagaita bude wuta bayan wata tattaunawar data hada da shugaban Chadi Idris Derby.
Wani baban mukarabin shugaban Najeriya, Hassan Tukur ya fadawa Muryar Amirka cewa yan yakin sa kan sun amince bisa ka'ida cewa zasu sako yan matan.
A wani labarin kuma, kungiyar lafiya ta Duniya tace Najeriya, ta tsira daga zazzabi Ebola, bayan data shafe kwanaki arba'in da biyu ba tare da bada rahoton wani ya kamu da cutar ba.
Yau litinin wani wakilin kungiyar lafiya ta duniya mai suna Rui Gama yace wannan labari ne mai faranta rai.
Mutane ashirin ne suka kamu da Ebola a Nigeria, kuma takwas daga cikin wannan adadi ne cutar ta kashe a zaman wani bangare na bular anobar kwayar cuta mafi muni da aka gani.
A makon jiya kungiyar lafiya ta duniya ta ayyana cewa kasar Senegal ta tsira daga cutar Ebola.

XS
SM
MD
LG