Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Giorgos Karagounis ya Shiga Cikin Masu Kula da 'yan Kwallon Greece


Greece's Giorgios
Greece's Giorgios

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Greece ta ce ta cimma yarjejjeniyar, da tsohon kaftin Giorgos Karagounis, na kasancewa daya daga cikin masu kula da kungiyar kwallon kafar kasar ta Greece.

Dan wasan tsakiyan ya kawo karshen zamanin sa da nasarori kamar cin kofin zakaru na nihiyar Turai.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Greece, a yau din nan, ta ce dan shekaru 37 dan wasan tsakiyan zai yin aiki tare da sabon mai kula da ‘yan wasan kasar ta Greece Koch, Claudio Ranieri, amma, tace zata fito da tsari dangane da sabon matsayin sa.

Dan wasan tsakiyan ya doka tamaula a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, wadda aka buga a kasar Brazil a bana din nan, inda suka sha kashi, a hannun Costa Rica a bugun daga kai sai gola.

Babu tabas ko zai ci gaba da buga kwallon bayan gasar wasa na biyu a kulob din Fulham, a shekaran da ta wuce.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG