Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Drogba Yayi Farin Cikin Cin Kwallon da Eden Hazard Yayi.


Dan wasannan Drogba ya gode ma abokin wasan shi Eden Hazard bayan cin kwallon farko da yayi bayan dawo warshi na biyu a kungiyar ta Chelsea.

Shi dai dan wasan na kasa-da-kasa ya bar kungiyar ne a lokacin kakar wasan zakaru na UEFA a shekarar 2012 wanda kungiyar Bayen Munich ta lashe wasan.

Kuma bayan dawowarshi a wannan kakar, ya dawo da irin wasanshi na yau da kullun a inda zai nuna bajintarshi a filin wasa na Stanford Bridge a ranar kowace Talata lokacin wasa na group G.

Drogba ya gayama gidan talabishin na ITV cewar, gama wasa da bugun daga kai se gola, kuma da fara wani sabon wasa da bugun daga kai se gona abu ne me kyau.

Ya kara da cewar ina da sa’a da yadda mukayi wasan mu, munci kwallaye biyu a farkon wasa, kuma ba mu tsayaba wanda shi ya haifar da nasarar da muka samu yanzu.

Shi kuwa dan wasannan Hazard shi yafi kowa buga ma kungiyar Charlsea bugun da ga kai sai gola a yan kwanakinnan. Amma shikuwa Drogba ya sauka daga kungiyar kasa-da-kasa ta Belgium ne don ganin kanshi ya baiwa dan wasannan damar gama wasanshi na 7.

XS
SM
MD
LG