Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Doke Afirka ta kudu Shine Abun yi


Koch din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, ta Najeriya, Steven Keshi, yace yanzu ya zama wajibi kungiyar, ta lashe wasan da zata buga da kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu, a wannan laraban mai zuwa.

Kungiyar ta Super Eagles a karshen makon daya gabata ta sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta Congo, inda ta nakadawa Najeriya kashi a gida, da ci 3 da 2.

Kungiyar kwallon kafa da Afirka ta kudu, ita take kan gaba a rukunin A, bayan da ta yiwa kungiyar kwallon kafa ta Sudan Kacha-kacha da ci 3 da babu, a wasan da suka buga a ranar juma’a.

Koch keshi, yace Brazil tayi rashin Nasara inda ta sha kashi da ci 7 da 1, Najeriya, ma an doke ta ranar asabar, yace ba lalle bane mu lashe duk wasanin mu, ko da yake banji dadin wasan da muka buga ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG