Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Vanguard Tayi Kira ga Atiku ya Janye Neman Takara ya Barwa janar Buhari.


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

A Najeriya wata kungiya mai suna Buhari Vanguard ta gudanar da taron manema labari inda ta bukaaci tsohon mataimakin shugaban kasar najeriya Alhaji Atiku Abubakar daya janye neman takarar daya keyi yabar Janar Muhammadu Buhari, saidai a gefe guda masu goyon bayan turakin Adamawan Atiku Abubakar sunce wannan batun ya janye daga takara ba mai yiwuwa bane.

Wannan kungiyar dai mai suna Vanguard mai fafutakar kare muradin janar Mohammadu Buhari, ta gudanar da taron manema labarai a Bauchi inda ta bukaci turakin Adamawa Atiku Abubakar daya janye neman takararsa ya barwa Buhari, Umar Ibrahim Tafida shine mai gudanar da wannan taron yakuma bayyana dalilansa kan wannan batu inda yace, “makasudun kiran wannan taro shine muna kira ga Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma wanda yanzu haka ya sayi form na neman tsayawa takara a wannan jam’iyya ta APC a kancewa ya janye ya barwa tsohon shugaban kasa janar muhammadu Buhari akan dalilai masu yawa damuka rubuta masa wasika arubuce.”

A bangaren magoya bayan Turakin Adamawa kuwa sunce wannan maganar ba mai yiyuwa bace, mukarrabin Turakin Adamawa Shehu Buba Umar yace, “wa‘yannan da suka rubuta wannan takardar abu biyune ko basu san tarihi ba kokuma sun manta, kuma indai a babin adalcine in suna maganar adalcine ai a jam’iyyar APC a yanzu cikin mutanen da suke neman shugabancin kasar nan babu wanda yafi cancanta ya janye ya hakura irin Muhammadu Buhari.” Wakilinmu ya tambayeshi meyasa ya fadi haka, sai ya kara dacewa, “na farko janal Buhari ya tsaya takara shekara ta 2003, yakuma tsaya 2007, sai 2011. Kuma lokacin daya tsaya takara ta shekara 2011 yace yana gabatar da kansa na karshe kenan bazai sake tsayawa ba, to a matsayinsa na dattijo bai kasance mai magana daya ba.”

Wannan shine kadan daga cikin bayanai daga masu goyon bayan buhari da kuma na Turakin Adamawa.

XS
SM
MD
LG