Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba'a Fara Tattaunawa kan 'yan Matan Chibok ba Kamar Yadda aka zata


Ba'a fara tattaunawar neman kubutar da 'yan matan Chibok fiye da 200 ba a yau Talata kamar yadda aka zata, ko da yake wasu alamu na nuna cewa 'yan Boko Haram da gwamnatin Najeriya na shirin tattaunawa a kasar Chadi.

Wata fitacciyar jaridar Najeriya mai suna This Day, ta buga labari a yau Talata cewa wata tawagar jami'an gwamnatin Najeriya da za'a yi tattaunawar da su, sun tafi N'Djamena babban birnin kasar Chadi.

A halin yanzu kuma, wani wanda ake cewa wai shugaban kungiyar Boko Haram ne, mai suna Danladi Ahmadu ya shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa shi ma za shi Chadin ya jira lokacin da za'a fara tattaunawar.

Hassan Tukur, babban jami'in fadar shugaban kasar Najeriya ya shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa babu wanda ya ce ga ranar da za'a fara yin tattaunawar, ko dayake sabanin hakan wani jami'in fadar shugaban na Najeriya, Doyin Okupe ya ce Talata za'a fara.

Gwamnatin ta dora alhakin kai hare-haren kan 'yan daidaikun mayakan Boko Haram, a yayin da Danladi Ahmadu yace 'yan fashi da makami ne suka kaiwa Damboa hari a ranar Lahadi.

XS
SM
MD
LG