WASHINGTON, DC —
Wata babbar kotu a Kano karkashin jagorancin mai shari’a Dije Aboki ta bada umarnin tsare wani basarake a Kano a gidan kurkuku,
Hakan ya biyo bayan tuhumar da a kewa basaraken na badda sawun wasu kudade har Naira miliyan ashirin da matasan da saura aluman garin Tsangaya a karamar hukumar Albasu a jihar Kano suka tara.
Kudaden dai an tara ne da niyyar kafa Bankin bada rance ga masu kananan sana’oi a wani mataki na yaki da talauci, a tsakanin jama’ar yankin.
Hukumar ta EFCC, ta sanar da kotun cewa kasancewa Aliyu Sulaiman Tsangaya, ma’aikacin daya daga cikin bankunan kasuwanci, dake Najeriya, sai alumar yankin suka bude ajiya a wannan bankin da yake aiki domin danka amanar kudaden a hannun sa.