Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An shiga Mako Na Biyu Na Gasar NPFL 2016/2017 A Najeriya


A Yayin da ake mako na biyu a gasar firimiya lig 2016/2017 ta tarayyan Najeriya a yau an fafata wasanni har guda goma a jihohi daban daban na kasar inda Kungiyar kwallon kafa ta Sunshine, tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Shooting Stars.

Plateau United ta lallasa Eyimba da ci 3-1, Gombe United ta samu nasara akan Remo Starts daci 2-1, Abia Warriors ta doke Katsina United da kwallo 2-0. Har ila yau kungiyar Nasarawa United tayi canjaras 1-1 tsakaninta da Enugu Rangers, El-kanemi ta tashi 0-0 da Wikki Tourist.

Akwa United nada 1 Rivers united nada 1, Niger Tornadoes a gida tayi kunnen doki da ABS Fc, Ifeanyi Ubah ta casa MFM Fc da kwallaye 4-1

Lobi Starts ta samu Nasara akan Kano Pillars da ci 1-0.

A yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ke jan ragamar teburi da maki shida.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG