Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Iyaye Da Laifin Sayar Da Diyar Su Domin Kudin Haya


A ranar Laraba data gabata rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta bada sanarwar cafke wasu iyaye bisa zargin kama su da laifin sayar da diyarsu mai shekaru shidda da haihuwa a kan kudi Naira dubu dari hudu, 400,000.

Mujallar Daily Trust ta wallafa cewar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Hafizu Inuwa, ya bayyana wa manema labarai cewar sun sami nasarar kama ma’auratanne a karamar hukumar Ikon, sakamakon bayanan sirri da suka samu.

Inuwa, ya bayyana cewa ma’auratan sun sayar da diyar tasu ne domin su sami kudin biyan haya sa’annan kuma su bude karamin shago domin zuba jari.

Ya ce, “ ranar 26, ga watan Afirilu , 2017, biyo bayan wasu bayanai da muka samu, mun sami nasarar kama ma’auratan George da uwargidansa Victoria, a sakamakon zarginsu da aikata laifin sayar da diyarsu akan kudi Naira dubu dari hudu, 400,000. Jami’an ‘yan sandan karamar hukumar ne suka damke wadannan mutane.

Hafizu, ya kara da cewa “a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike akan afkuwar lamarin a bangaren binciken muggan laifuka dake Calabar, babban birnin jihar Rivers, koda shike mahaifin ya musanta sayar da diyar tasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG