Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Kwamitin Kyautata Hulda Tsakanin Musulmi da Krista


 Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

An kafa Kwamitin kyautata hulda da dangantaka tsakanin mabiya addinai, a jamhuruyar Nijar.

Kwamitin dake karkashin ofishin, Ministan cikin gida na wani rangadi na wayar da kawunar jama’a, mabiya addinin Musulunci da Krista, dangane yanda zai gudanar da aiyukansa.

Burin wannan kwamiti shine hada kan Musulmi da Krista, domin gudanar da aiyuka kafada da kafada da shi wannan kwamiti, kuma duk abun da mabiyan zasu gudanar a cikin kasar sai sun shedawa kwamitin, domin yin sa cikin tsari.

Kwamitin Hulda Addini - 3'37"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

XS
SM
MD
LG