Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Baje Kolin Alkur’ani Mai Tsarki Na Tarihi A Birnin Washington DC


Gidan ajiye kayan tarihi Smithsonian
Gidan ajiye kayan tarihi Smithsonian

An soma wani gagarumin gwajin Alkur’ani mai tsarki a birnin Washington DC wanda kuma shine karo na farko da aka taba irinsa a Amurka

Wannan gwajin wanda aka bude a ranar 22 ga wannan nan na Oktoba, ya hado hancin muhimman tsofaffin rubuce-rubucen Kur’anin sama da guda 60, ciki harda wadanda aka wallafasu tun sama da shekaru Dubu da suka shige a sassan duniya daban-daban, kama daga Arewacin nahiyar Afrika, Turkiya, Iran da kuma Afghanistan.

Daga cikin abubuwan da ake nunawa har da wasu manyan allunan da aka rubuta da tawada mai launukka iri-iri.

Ana dai gudanar da wannan gwajin ne a zauren baje kayan tarihin na Smithonian dake nan Washington kuma shirin gwajin Alku’anin na hadin gwiwa ne tsakanin cibiyoyin tarihi na Amurka da na kasar Turkiya, musamman Cibiyar Tarihin Islama ta birnin Istanbul.

XS
SM
MD
LG